Jam’iyyar mai mulkin Kasa ta APC ta kaddamar da zababbun shugabannin jihohin kasar nan a jihohi 34 na kasar da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai ba a kaddamar da shugabannin jihohin Kano da Sokoto ba.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da babban taron kasa da aka sanya ranar 26 ga watan Fabrairu, duk da cewa jam’iyyar ta tabbatar da ranar gudanar da babban taron ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Da yake bayyana hakan a lokacin kaddamarwar, sakataren kwamitin riko, James Akpanudoedehe, ya ce an umarce shi da ya mika musu takardar shaidar dawowar su.