Hukumar Zaɓe mai zaman Kanta ta Jahar Enugu a ranar Alhamis ta sanar da sakamakon zaɓen Ƙananan Hukumomi da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022.
Ya bayyana cewa, ƴan takarar Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi guda 17 suka lashe kujerun, a yayinda Kansiloli 260 suma suka samu nasara a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Muna Karkashin Hari’, Daliban Najeriya Dake Ukrain Sun Roki Gwamnatin Tarayya Data Kwaso Su Zuwa Gida
Dayake bayyana sakamakon a hedikwatar Hukumar dake Enugu, Shugaban Hukumar Dr Mike Ajogwu ya bayyana cewar ƴan takarar su suka samu nasarar a ƙuri’un da aka kaɗa a dukkanin kujerun Jahar.
Dr. Ajogwu ya ƙara dacewa ƴan takarar Jam’iyar PDP sun samu sama da kashi uku a dukkanin mazaɓun da aka yi zaɓe a yankunan.
Ya bayyana cewar, an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da adalci, kuma an gudanar dashi kamar yadda dokar kananan hukumomi ta Jahar Enugu.
Dayake bada takardun shaidar zaɓen Shuwagabannin, Shugaban Hukumar yace takardun Kansiloli na shaidar sun lashe kujerun za’a basu a kananan hukumomin su.
Comments 1