By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar PDP ta sake sanya ranar tantance masu neman tsayawa takara a babban zaben 2023.
Jam’iyyar ta kuma maida taron kwamitin zartaswar jam’iyyar na kasa (NEC) da aka shirya gudanarwa tun a ranar 5 ga watan Mayu zuwa ranar Talata 10 ga watan Mayu.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakatarenta na kasa Sen. Samuel Anyanwu ya fitar.
Ya ce ranar da ta gabata ta ci karo da zaben wakilan kananan hukumomi wanda ya hada da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar, inda ya ce an yi nadama kan duk wani abin da ya same su.
Anyanwu ya ce an shirya gudanar da taron ne a sakatariyar kasa dake Wadata Plaza Abuja.
Kazalika, kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa (NWC) ya kuma sake dage ranar tantance duk masu neman takarar gwamna da shugaban kasa daga ranar Talata 3 ga watan Mayu zuwa Laraba 4 ga watan Mayu.
Jam’iyyar a wata sanarwa ta daban ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Mista Debo Ologunagba, a Abuja a daren ranar Litinin, ta ce an yi gyara a ranar ne sakamakon bikin Salla karama.
“NWC ta nemi afuwar duk wata matsala da wannan canji na kwanan wata zai iya haifarwa,” in ji Ologunagba.
(NAN)