Jam’iyyar PDP ta soke sakamakon taron wakilan jam’iyyar na jihar Ekiti a ranar 15 ga watan Janairu, 2022.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a daren ranar Litinin, inda ya ce za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamnan Ekiti ta hanyar amfani da jerin sunayen wakilai.
A ranar Laraba ce dai za a gudanar da zaben fidda gwanin.
Ayu ya yi kira da a gaggauta janye duk wani mataki na kotu da bangarorin da ke rikici da juna suka kudiri aniya
A cewarsa, matakin da shugabannin jam’iyyar suka dauka ya zama dole a kan duk masu ruwa da tsaki a jihar Ekiti.
A baya dai jam’iyyar ta zabi wakilai na wucin gadi mai mutum uku da za su zabi dan takarar PDP a zaben gwamnan da za a yi a watan Yulin shekarar 2022.