Tun bayan fara yin ƙwallon ƙafa akwai haziƙan ‘yan wasan da suke jefa ƙaallaye kamar kamar ruwa idan suna wakiltar ƙasarsu a gasa daban-daban, kama daga gasar cin kofin duniya dama sauran gasar nahiyoyinsu.
Akwai jerin ‘yan wasan da suka fi yawan jefa ƙaallye wa ƙasar su ta haihuwa inda sunayensu ya shiga kundin tarihi a dunuyar ƙwallon ƙafa.
Saidai daga cikin jerin ‘yan wasan akwai waɗanda basu taɓa lashe gasar cin kofin duniya ba inda wasu daga cikinsu sun lashe, haka wasu ma basu taɓa lashe wa ƙasarsu ta haihuwa wata gasa ba amma sun jefa ƙwallaye da yawa yadda ya kamata.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan kamar haka:
1. Ali Daei ɗan ƙasar Iran ya jefa ƙwallaye 109.
2. Cristiano Ronaldo na Portugal ya jefa ƙwallaye 101.
3. Mokhtar Dahari ya jefa ƙwallaye 86.
4. Ferenc Puskas ya jefa wa ƙasarsa ƙwallaye 84.
5. Godfrey Chitalu yaci guda 79.
6. Hussein Saeed ya jefa guda 78.
7. Pele ya jefa ƙwallaye guda 77.
8. Kunishige Kamamoto ya jefa 75.
9. Bashar Abdullah ya jefa guda 75.
10. Sunil Chhetri ya jefa ƙwallaye guda 72.