Jihar Bauchi Ta Ɓullo Da Tsarin Hana Amfani Da Tsabar Kuɗi Don Yakar Cin Hanci Da Rashawa
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya tsarin rashin amfani da tsabar kudade wajen hada-hada domin magance matsalar cin hanci da rashawa a harkar ilimi a jihar.
Gwamnan jihar Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana haka a wajen bude taron kwana biyu na ilimi da aka gudanar jiya a sansanin Sultan Sa’ad Abubakar Hajj Camp dake Bauchi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ɗaukar aikin bogi: Sama da ƴan Najeriya 1,000 ne suka makale a Burtaniya – IOM
Ma’aikatar ilimi ta jihar ce ta shirya taron, ana sa ran za ta samar da matakan da za a magance tabarbarewar ilimi a jihar wanda ya bijirewa kokarin gwamnatocin baya.
Gwamna Mohammed ya ce cin hanci da rashawa ya dade yana hana ci gaban ilimi a jihar. “Mun aiwatar da tsarin zamani kamar tsarin rashin amfani da tsabar kuɗi da kuma canja wurin yanar gizo don duk biyan kuɗi da suka shafi ilimi. Wannan yana rage musayar kuɗi wanda zai iya haifar da sata ko karkatar da kudade.
“Bugu da ƙari, wannan ba wai kawai yana tabbatar da ingancin hada-hadar kuɗi ba har ma yana ba da damar azabtar da mutanen da suka aikata ba daidai ba,” in ji shi.
A wani labarin kuma:Bamu da wata yarjejeniya da Tinubu – NNPP
Shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa jam’iyyar ta kulla yarjejeniya da shugaban kasa Bola Tinubu a yunkurin ci gaba da zama a jihar.
Hasashen ya biyo bayan ganawa da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da Tinubu suka yi a fadar shugaban kasa.