Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya ce siyasantar da harkar tsaro zai kara tsunduma jihar ne cikin rudani, don haka dole kowa ya iya bakin shi.
Abdul’aziz Yari wanda yake zantawa da yan jaridu a mahaifar shi ta Talata Mafara ya bayyana bukatar hada karfi da karfe wajen ganin an kawo karshen matsalar.
“Matsalar tsaro matsala ce da ta fi karkata ga bangaren gwamnatin tarayya wacce dole sai an bi wasu dabaru tare da samun goyon baya daga jiha, don haka ya kamata a samu shawarwari masu nagarta ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari don ganin an dakile miyagun ayyuka a kasar nan, cewar Yari.
Ya kara da cewa dole ne gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin ba a ragar ma kowa ba kama daga yan fashin daji da ma duk wani mai hannu dake tallafa musu.
Da yake tsokaci kan dokar haramta hakar ma’adinai da Shugaba Buhari ya yi, Abdul’aziz Yari ya ce kai tsaye ba za a iya danganta matsalar tsaro da hakar ma’adinan ba dole sai an zurfafa bincike.