“Jihohi 19 ka iya fuskantar barazanar Ambaliyar ruwa a Najeriya” ~ SEMA
Hukumar NEMA ta yi gargadi akan yiwuwar samun ambaliya a yankuna 56 daga Jihohi 19 a Najeriya sakamakon mamakon ruwan sama.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA, ta yi gargadin cewa jihohi 19 da suka ƙunshi yankuna 56 a fadin Najeriya na fuskantar hadarin samun ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da mummunar ambaliya a cikin wata mai zuwa.
Kodinetan Hukumar na yankin Legas, Mista Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta NEMA ta zo ne a matsayin tunatarwa kan barazanar Ambaliya da yawan ruwan sama ke haifarwa a lokacin damina.
Yankunan da aka bayyana a cikin sanarwar da za su iya fuskantar barazanar sun haɗa da Jihar Delta wato kusa da Aboh, da Jihar Ekiti tare da babban birnin ta Ado Ekiti, sai Jihar Ondo wadda ta ƙunshi yankunan Akure, da Idanre, da Ifon, da Iju Itaogbolu, da Ogbese, da Owo, da Owena da kuma cikin garin Ondo.
A Jihar Legas kuwa, kamar Apapa, da Badagry, da Eti Osa, da Ikeja, da Ikorodu, da Ikoyi, da Lagos Island, da Ojo, da Surulere, sai Jihar Anambra da ya haɗa da yankin Atani, da Ogun, da Ifo, da Ota, da Sagamu, yayin da a Jihar Nasarawa yankuna irin su Lafia da Wamba, da kuma yankunan Ikom da Ogoja na Jihar Cross River duk suma cikin jerin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Uwargidan Shugaban Kasa Ta Karbi Bakuncin KKK Super Falcons
Haka ma Sanarwar ta shawarci Jihar Bauchi da ta kasance cikin shiri musamman a garin Jamaare da Misau da Azare da Itas da Kafin Madaki da Kari da Kirfi da Tafawa Balewa da kuma Katagum. Sai a Jihar Jigawa da ta haɗo da garin Haɗejia da Miga. Yayin da Jihar Osun ta ƙunshi yankunan Ilesa da Osogbo.
Kosubosu ta Jihar Kwara na ciki, sai Anka da Bungudu da Gusau na Jihar Zamfara, sai Goronyo ta Jihar Sokoto, da Numan da Shelleng na Jihar Adamawa, sai Serti ta Jihar Taraba, da kuma Ito da Katsina-Ala da Vande-Ikya duk suna cikin yankunan da aka bukaci su dauki matakan kariyar.
Haka kuma an shawarci yankunan Oguta da Orlu na Jihar Imo, sai garin Ugba na Jihar Abia da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana saboda hasashen ruwan sama da aka yi da kuma yiwuwar samun ambaliya.
Gargadin na hukumar NEMA ya zama muhimmiyar tunatarwa ga mazauna yankunan da kuma hukumomin da abin ya shafa da su tashi tsaye wajen kare rayuka da kuma duniyoyin al’umma.
A wani labarin kuma:Uwargidan Shugaban Kasa Ta Karbi Bakuncin KKK Super Falcons
Gwamnan ya kuma kara jaddada shirin gwamnatinsa na hada hannu da hukumomin tsaro da ke jihar domin ganin tsaron al’ummar jihar ya kyautatu.