By Abbas Yakubu Yaura
Adadin wadanda suka mutu sakamakon zazzabin Lassa ya karu zuwa 99, in ji Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya.
Wannan dai ya zo ne kamar yadda cibiyar ta bayyana cewa kawo yanzu ba a samu rahoton bullar kamuwa da cutar a kasa da mutane 4,482 ba.
“A cikin dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, an samu kashi 84 cikin 100 a jihohin Edo, Ondo da Taraba,” in ji cibiyar a sabon rahoton cutar zazzabin Lassa da aka buga ranar Juma’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa zazzabin Lassa cuta ce wadda take yaduwa a Najeriya a duk shekara amma ana samun karuwar masu kamuwa da cutar a lokacin rani.
Cibiyar ta kara da cewa mutane 4,482 da ake zargin sun kamu da cutar sun fitone daga daukacin jihohi 36 na tarayya da aka samu bullar cutar da kuma babban birnin tarayya.
Hukumar NCDC ta lura cewa a shekarar 2019, an samu jimillar mutane 796 da suka kamu da cutar, yayin da 1,165 aka tabbatar da kamuwa da cutar a shekarar 2020 a daidai lokacin da annobar ta sake barkewa.
Sai dai Darakta Janar, Dakta Ifedayo Adetifa, ya bayyana cewa cibiyar ta aike da wasikun gargadi ga jihohi domin sanar da su halin da ake ciki.
Cibiyar, a cikin wani sako a shafinta na yanar gizo, ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su “ci gaba da nuna shakku kan cutar zazzabin Lassa, su yi taka-tsan-tsan tare da lura da alamun cutar,” ta kuma kara da cewa “ba duk zazzabin cizon sauro ba ne.”
Comments 1