A yau Laraba Jami’an Ukraine sun bayyana cewa, Ministan kula da harkokin cikin gida na kasar na daya daga cikin mutum 16 da suka mutu a wani hadarin jirgin sama kusa da Kindergaten dake wajan birnin Kyiv. Kamar yadda CNN ta ruwaito.
A wani faifain bidiyo da aka yada a yanar gizo bayan faruwan lamarin, an jiyo ihun mutanen dake cikin jirgin yayin da ya ke ci da wuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Daure Wani Basarake Shekaru 8 a Gidan Gyaran Hali
Sai dai har kawo hada wannan rahoton babu cikakkun bayanai kan musabbabin hadarin jirgin
Kazalika daga cikin wadanda suka mutun, akwai Manyan Jami’ai daga Ma’aikatar cikin gida na kasar Ukraine da su ka hada Ministan Ma’aikatar Denys Monastyrsky da mataimakinsa Yevgeniy Yenin.
Kawo yanzu, Rahotanni sun nuna cewa, Akwai mutane akalla 22 da suka hadar da yara 10 a asibiti suna amsan kulawar likitoci.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi Mataimakin Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Majalissar Zartarwa Na Farko a 2023
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yanzu haka dai shine ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya na farko a shekarar 2023.
Taron wanda aka fara da ‘yan mintoci da karfe 10:00 na safe yana gudana ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.