Shugaba Joe Biden ya mayar da martani a ranar Laraba ga sanarwar da Donald Trump ya yi na sake tsayawa takara a fadar White House.
Biden ya bayyana cewa ‘yan jam’iyyar Republican sun “kasa” sun gaza ciyar da kasar gaba, yayin da suke kan karagar mulki.
KARANTA ANAN: CP Kolo Ya Ziyarci Kwalejin Fasaha Ta Kauran Namoda
“Donald Trump ya gaza wajen shugabancin Amurka,” in ji Biden a cikin wani sakon twitter daga Bali, inda ya halarci ranar karshe ta taron G20.
Wannan ya biyo bayan wani faifan bidiyo da Trump ya wallafa wanda yake bayyana aniyarsa.
Daga baya, yayin da suke halartar wani biki tare da sauran shugabannin G20, manema labarai sun tambayi Biden da shugaban Faransa Emmanuel Macron ko suna da martani game da sanarwar Trump.
Su biyun sun kalli juna a takaice Biden ya ce “ba da gaske ba,” yayin da Macron ya yi shiru.
A wani labarin kuma: Amurka: Donald Trumph Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takara A 2024
Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman shugaban kasa a jam’iyyar Republican a shekarar 2024.
Trump na neman komawa fadar White House bayan da ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2020 ya samu tsaiko daga Joe Biden.