Tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Jonathan ya taya shugaba Buhari murnar cikarsa shekaru 80 a duniya, ya kuma yi addu’ar Allah ya yi masa jagora ya kuma kare shi yayin da yake tafiyar da al’amuran kasa a sauran watannin gwamnatin sa.
A wani sakon fatan alheri da ya sanya wa hannu, Dr Jonathan ya bayyana cewa shugaba Buhari ya samu dama ta musamman na jagorantar kasar har sau biyu, a matsayin shugaban kasa na soja da kuma shugaban farar hula.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Bukukuwan Kirsimeti Da Sabuwar Shekara
Tsohon Shugaban ya bayyana cewa; “Na yi farin cikin taya ka murnar cika shekaru 80 da haihuwa. Ina taya ‘yan uwa da abokan arziki da sauran jama’a fatan alheri da yin godiya ga Allah bisa baiwar rayuwa da kuma karfin tafiyar da al’amuran wannan kasa tsawon shekaru bakwai da rabi.”
“A matsayinka na shugaba, kana daya daga cikin ‘yan Najeriya kalilan da suka samu damar gudanar da mulkin kasarmu a lokutan siyasa daban-daban; duk a matsayin shugaban kasa na soja da kuma shugaban farar hula. A cikin wadannan lokutan, kun ba da himma wajen cimma burin ku ga al’umma.”
“Yayin da kuke bikin, ina yi muku fatan alheri, zaman lafiya da kuma ikon Allah a cikin sauran watannin gwamnatin ku da ma bayan haka. A madadin iyalina, ina yi muku barka da zagayowar ranar haihuwa.”
A wani labarin kuma, 2023: Za Ku Fahimci Yadda APC Take Da Karfi A Ranar Zabe – Badaru Ga ‘Yan Adawa
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce jam’iyyun adawa za su fahimci banbancin jam’iyyar da jama’a suka zaba da kuma wadanda aka raina a zaben 2023.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga dimbin jama’a a karamar hukumar Kaugama.