Wakilinmu Mu’azzam Yakubu Sanka
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kirayi sabon shugaban masu rinjye na majalisar wakilan Tarayya, Hon. Alasan Ado Doguwa da ya zamo jajirtacce da cigaba da tafiya da kowa.
Gwamnan, a wata wasika da ya aikawa Shugaban masu rinjayen mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Alh. Usman Alhaji, wacce aka bayyanawa manema labarai.
Takardar ta ce zaban Hon. Alasan da akayi na daura shi kan wannan kujerar abune da ya dace bias la’akari da kasancewar sa a wajen gudanar da aiki da kuma kasancewar sa daya daga cikin ‘yan majalisar da suka dade ana damawa da su.
Wasikar ta kammalu da yiwa sabon Shugaban masu rinjayen murnar samun wannan matsayi da kuma Addu’ar Nisan kwana tare da yiwa al’umma aiki tukuru.