Kaduna: Gwamna Uba Sani ya ɗauki ɗamarar ceto duk daliban da aka sace a Kuriga
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alkawarin ceto dukkan daliban da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ranar Alhamis.
A ziyarar da Gwamnan ya kai wa al’ummar yankin domin jajantawa al’umma kan lamarin, Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar yankin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da kuma mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dalilin da yasa Dubai taƙi ɗage haramcin baiwa ƴan Najeriya biza – Gwamnati
Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da adadin yaran da aka sace ba, Sani ya bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da hada kai da gwamnati wajen ganin an sako yaran.
Ya kuma bayyana cewa za a kafa kwamitin tsaro a Kuriga tare da neman a kafa sansanin soji a yankin domin karfafa tsaro.
“Za a kafa kwamitin tsaro a Kuriga, wanda za a samu mambobi daga manyan masu ruwa da tsaki a al’ummar Kuriga, Hukumomin tsaro, da kuma Gwamnatin Jiha.
Sani ya kara da cewa “Zan gabatar da kakkausar murya ga babban hafsan hafsoshin tsaro da kuma babban hafsan soji na kafa sansanin soji a Kuriga domin karfafa tsaro a yankin.”
NAN ta ruwaito cewa gwamnan a wata sanarwa daga baya, ya ce lamarin na Kuriga ya karfafa bukatar ‘yan sandan jihar.
“Wannan lamari mara dadi na Kuriga yana karfafa matsayin mu na goyon bayan kafa ‘yan sandan Jiha.
“Tare da ‘yan sandan Jiha, za a samu rundunar ‘yan sanda a Kuriga da ta fito daga ’yan uwa da suka fahimci yanayin kasa, jama’a da kuma al’amuran da ke faruwa.
“Suna iya tattara hankali cikin sauƙi. Haka kuma tsarin mulkin kasar zai ba su ikon rike makamai, ciki har da na zamani.
“Wannan yana da mahimmanci saboda ba a yarda kungiyoyin ‘yan banga su dauki makamai.
Ya kara da cewa “Koyaushe suna cikin jin kai daga wadannan masu aikata laifukan da ba su mutunta rayuwar dan adam.”
A wani labarin kuma:Sojoji sun lalata hedkwatar kungiyar IPOB, ESN
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dakarun sojin Najeriya, suka yi nasarar fatattakar wani hedikwatar koli ta masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB da kuma bangaren tsaro na kungiyar tsaro ta Gabas, ESN.
Hedikwatar rundunar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X yayin da take ɗora hotunan abubuwan da ta samu nasarar ƙwatowa.