Kaduna ta tura Malamai 2000 a Makarantu 155 domin inganta Ilimin Ƴaƴa Mata
Gwamnatin jihar Kaduna ta tura malamai 2000 a makarantu 155 dake fadin kananan hukumomi 23 na jihar a wani mataki na magance matsalolin ilimin yara mata a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Obi ya musanta fitar da ƙudirorin sa nason zama Shugaban Ƙasa
Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a lokacin da take jawabi a wajen wani horo da shirin inganta ilimin ƴaƴa Mata na AGILE a karkashin ma’aikatar ilimi, tare da hadin gwiwar hukumar kula da ayyukan malamai a jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta shirya.
Yunƙurin yana da nufin tabbatar da cewa an ba wa yarinya duk wata dama don cimma cikakkiyar damarta.
A wani labarin kuma: Babban hadimin Gwamnan Jihar Kwara yayi murabus makonni bayan tarbar Saraki
Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kwara Musbaudeen Esinrogunjo na musamman kan harkokin karkara ya yi murabus daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.
Murabus din nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa yana shirin komawa jam’iyyar adawa ta PDP.
Kimanin makonni biyu da suka gabata, Esinrogunjo ya tarbi shugaban jam’iyyar adawa a jihar kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, a ofishin yakin neman zabensa, lamarin da ya janyo farin jini a jam’iyyar PDP.
Sai dai matakin ya sa mataimakin gwamnan, Mista Kayode Alabi, ya kai masa ziyara sa’o’i kadan bayan tafiyar Saraki, inda magoya bayan jam’iyyar APC suka makale a ciki domin nunawa ‘yan adawa cewa har yanzu yana nan a APC.
Sai dai a cikin wasikar murabus din da Daily Trust ta gani a ranar Litinin, Esinrogunjo ya bayyana cewa ya yanke hukuncin ne saboda wasu dalilai na kashin kansa, ya kuma gode wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da ya ba shi damar yin aiki.