Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Wakilai, a ranar Talata ya taya zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, murnar cikarsa shekaru 71 a duniy, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Gbajabiamila a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce Tinubu ya nuna kimar dimokaradiyya tsawon shekaru kuma ya kamata ‘yan Najeriya masu kishin kasa su yi bikin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Wakilai Ta Yi Jimamin Rasuwar Diya, Ta Kafa Tawaga Don Kai Ziyartar Ta’aziyya Ga Iyalansa
Ya bayyana Tinubu a matsayin jarumi kuma mai kishin al’umma mai adalci, kuma “mai son jama’a.
Dan majalisar ya kuma ce ya ji dadin yadda Tinubu ya cika burinsa na zama shugaban Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ina taya zababben shugaban mu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 71 da haihuwa.
“Dukkanmu mun gode wa Allah da ya ba wa zababben shugaban kasa rai, kuma muna addu’ar Allah Ya ci gaba da ba shi lafiya domin cimma burinsa na ganin Najeriya ta inganta.”
A wani labarin kuma, Karshen Tika-Tika-Tik: Ortom Ya Dauki Kaddarar Shan Kaye A Zabe, Ya Janye Kara
A karshe gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya amince da sakamakon zaben Sanatan Benue na Arewa maso Yamma da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Idan za a iya tunawa cewa, Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Ortom na jam’iyyar PDP wanda ake sa ran zai kammala wa’adinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayu, ya tsaya takarar Sanata amma ya sha kaye a hannun Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC.