Kamfanin Ɗangote ya ƙaryata kai samamen EFCC a ofishin sa na Legas
Kamfanin Ɗangote ya ƙaryata batun kai samame a babban ofishin kamfanin da ke Legas, wanda suke tunanin cewa labarin ƙaryar ya taɓa daraja da martabar kamfanin.
Kamar yanda akayi ta yaɗa rahotannin zuwan Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa ta EFCC babban ofishin mu dake Jahar Lagos a ranar 4 ga watan Janairun 2024, mun fahimci irin karsashin da abokan hulɗar mu da kuma sauran al’umma suke dashi domin sanin haƙiƙanin abinda ya faru, hakan ne yasa zamu sanar al’umma abinda ya faru.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shuwagabannin hukumar gudanarwar kamfanin, a cikin wani saƙo da suka fitar domin ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa EFCC ta kai samame a babban ofishin na Legas.
A ranar 6 ga watan Disamba,2023 mun samu wasiƙa daga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da rashawa ta ƙasa wato EFCC, inda suka buƙacemu mu basu ba’asin Kuɗaden ƙasashen waje wato Dalar Amurka da Babban Bankin Najeriya ya bamu daga shekara 2014 zuwa yanzu. Mun fahimci cewa ba mu kaɗai aka baiwa wannan wasiƙar ba, an turawa wasu kamfanonin kimanin 51 kuma suma ana neman wannan bayanan daga gare su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kamfanin Ɗangote ya ƙaryata kai samamen EFCC a ofishin sa na Legas
Mun baiwa Hukumar EFCC takardar karɓar buƙatar da suka turo mana, muka kuma buƙaci su yi mana ƙarin bayani a ɓangaren da suke buƙatar bayanin, ko kuma daga wane ɓangare na rukunin kamfanonin mu. Mun kuma buƙaci ƙarin lokaci domin haɗawa tare da gabatar musu takardun da suka kai shekaru goma.
Haka Kuma, hukumar EFCC basu fayyace mana ɓangaren da suke da buƙatar bayanan ba, kuma basu bamu damar da muka bukata daga gare su ba dangane da karin lokaci, suka kafe akan lallai suna da bukatar wannan bayanai a kurarren lokaci. Duk da wannan ‘sa toka sa katsin’ da akayi, mun tabbatarwa hukumar EFCC cewa zamu gabatar musu da bayanan da suka buƙata a lokuta daban daban saboda muna kan kamala tattara bayanan.
A ranar 4 ga watan Janairun 2024, ma’aikatan mu suka fara miƙawa Hukumar EFCC rahoto kashi na farko. Baya ga haka, Jami’an hukumar EFCC suka ƙi karɓar takardun rahoton da muka gabatar musu, suka ƙi amincewa da kai musu da akayi, suka ce sai dai suzo ofishin mu su karɓi wannan kwafin rahoton da muka gabatar musu da kansu.
Duk da kasancewar ma’aikatan mu suna ofishin su da takardun bayanan da suka bukaƙata, wasu daga cikin jami’ansu suka wuce zuwa ofisoshin domin karɓar wannan rahoton da aka gabatar musu wanda hakan ya zubar mana da ƙima da kuma taba darajar mu. Duk da yake jami’an nasu basu dauki wasu takardu ko kuma wani kundi daga ofishin namu ba alokacin zuwan nasu, domin duk abinda suke nema yana ofishin su.
Muna faɗa da babbar murya cewa, babu wani zargi ko kuma wata badaƙala da ake zargin daya daga cikin rukunin kamfaninnikan mu da ita a wannan lokacin, face dai muna bayar da bayanan da aka buƙata daga gare mu domin taimakawa hukumar EFCC a binciken da take yi.
A matsayinmu na kamfanin da yake biyayya ga dokokin ƙasa, a shirye muke da mu bada haɗin kai wajen baiwa hukumar EFCC duk wani bayani da suke da buƙata daga wajen mu. Mun riga mun miƙa musu kason farko na bayanan da suka buƙata daga gare mu, muna kuma aiki tuƙuru domin ganin mun basu sauran bayanan da suka rage daga gare mu akan lokaci, domin taimakawa binciken da suke yi.
Gamayyar Kamfanonin mu suna daga cikin waɗanda suka fi bada gudunmawa wajen bunƙasar tattalin arziƙin kasar nan, kuma daya cikin manyan kamfanonin dake cikin kasuwar hanneyen jarin ƙasar nan, sannan kuma ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da suka fi biyan haraji mai yawa a kasan nan. Mun kasance masu biyayya ga dokokin ƙasa tare da kare martabar ta a yunkurin da gwamnatin tarayya take yin a ganin an samar da bunƙasar tattalin arziƙi ta yanda masu zuba hannayen jari na gida dana waje zasu sami damar yin hakan.
Muna kira ga abokan hulɗarmu su fahimci yanda abin yake, su kuma kwantar da hankalin su. Zamu ci gaba da sanar dasu duk halin da ake ci lokaci zuwa lokaci.