Kamfanin Google ya bayyana shafukan Shaƙatawa 15 da ƴan Najeriya suka fi ziyarta
Kamfanin Google ya bayyana shafukan da akafi ziyarta na tsawon shekara ɗaya data gabata daga ƴan Najeriya, domin bikin cikar Google Street view shekaru 15 da aka ƙaddamar a Shekarar 2012.
Shugaban Sashen Sadarwa da Hulɗar Jama’a Na yankin Yammacin Afirka Taiwa Kola-Ogunlade ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis a Lagos.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Fargaban Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Yar Faransa A Kusa Da Bakassi
Mr Kola-Ogunlade ya lissafo adireshin da ƴan Najeriya suka fi ziyarta da suka haɗa da Wuraren Shaƙatawa, da tarihi da Manyan Makarantu da sauran su.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya bada rahoton cewa Manhajar Google Street view an faɗaɗa ta, ga sama da Ƙasashe 100 da yankunan su a fadin duniya.
Google Street view ya Kasance yana ɗauko hoto na sama da miles miliyan 10 na hotuna, da zai iya zagaye duniya sau 400.
Yace shafin da aka fi ziyarta a Najeriya a tsawon shekara ɗaya shine wajen hutawa na Oniru Beach Resort, sai Elegushi Royal Beach da Wurin Shaƙatawa na Marwa Beach dukkanin su a cikin Lagos.
Mr Kola-Ogunlade ya Ƙara dacewa Wurin Tarihi ba garin Benin, Jahar Edo daya shafin Masarautar Benin na daga cikin shafin da aka fi ziyarta a Najeriya na tsawon shekara ɗaya.
A cewar sa, sai wurin tarihi na yaƙin da akayi na Umuahia Jahar Abia, wanda yake bayyana yadda aka gudanar da yaƙin Farar Hula na Najeriya-Biafra.
“Sai na uku shine wurin Tarihi a Kalakuta Dake Ikeja, Jahar Lagos wanda ke ɗauke da Kayan tarihin Sarkin Afrobeat, Fela Kuti.
“Sai cibiya dake Lekki da wani wuri da akafi sani da Bariga Waterfront Jetty sune na uku da akafi ziyarta a Ƙasar, masu kayayyakin ban sha’awa.
“Sai wuraren da ƴan Najeriya ke yawan ziyarta shine Shafin Jami’ar Ibadan ta Jahar Oyo, da Jami’ar Jaha ta Benin dake Jahar Edo”, Inji shi.
Yace a faɗin duniya, Burj Khalifa Dake Dubai shine shafin da akafi ziyarta, sai manyan gine-gine na Eiffel Tower Dake Paris, Ƙasar Faransa da kuma Taj Mahal, India.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa yace manufar Kamfanin Google shine su shirya wani ɓangare na samar da bayanai a faɗin Duniya tare da samun su cikin sauƙi.