Kamfanin jirage saman Ethiopian Airlines zai cigaba da jigila zuwa yankin Tigray dake arewcun kasar a gobe laraba. Kamar yadda RFI ta ruwaito.
Kamfanin jiragen ne ya sanar da hakan a sanyin safiyar yau Talata, wanda hakan zai zama aikinsa na farko cikin watanni 18 tun bayan barkewar yakin basasa a Habasha.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na Dakatar Da Haihuwa Haka, a Cewar Wani Mai Mata 12 Da ‘ya’ya 102 Da Kuma Jikoki 568
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan wakilan Gwamnati da na fararan hulla sun ziyarci Mekelle domin tabbatar da yarjejeniyoyin da aka cimmawa na zaman lafiya a watan da ya gabata.
Yarjeniyoyin da suka hadar da, Alkalwarta mai da hanyoyin sadarwa a yankin, sun kawo karshen gwabza kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati da mayakan Tigray da yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane da raba milliyoyi da muhallansu.
Idan ba amanta ba, Gwamnatin Habasha da Yan tawayen Tigray sun cimma matsaya kan dakatar da yakin ne a ranar 2 ga watan Nuwanban shekerar nan, a wani taro da aka yi a kasar Afrika ta kudu tare da sanya hannu kan yarjejeniyar a Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Sai dai kuma an sake fara zirga-zirgar jiragen sama na wani dan lokaci bayan da dakarun gwamnati suka kwace garin Mekelle, babban birnin yankin Tigray, amma an sake dakatar da shi bayan da sojojin Tigray suka kwace birnin.
A wnai labari kuma, Tinubu Da Peter Obi Sun Magantu Kan Wata Kisan Lauya
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun yi Allah wadai da kisan wata lauya yar jihar Legas, Omobolanle Raheem, da wani dan sandan ya yi a unguwar Ajah dake jihar a ranar Lahadi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Omobolanle ta fito ne daga wani gidan cin abinci tare da wasu ’yan uwanta a ranar Kirsimeti lokacin da dan sandan mai suna ASP Drambi Vandi ya harbe ta.