Kanin Haliru Jika, dan takarar gwamna na jam’iyyar, NNPP, a jihar Bauchi, Buhari Jika, da wasu ‘yan uwansa sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP, Daily Post ta rawaito.
Wadanda suka sauya sheka suna goyon bayan takarar Gwamna Bala Mohammed ne a karo na biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Ta Samu Kudin Shiga Tiriliyan N1.3tn da Dala Biliyan $4bn Daga Kadarori 54 Da Akayi Watandarsu
Har ila yau, wanda ke ba wa jam’iyya mai mulki kwarin gwiwa a jihar sun hada da Ko-odinetan yakin neman zaben tsohon Gwamna Mohammed Abubakar, Auwalu Ganjuwa, da shugaban kungiyar ‘yan takara na jihar, Abbas Barde.
Sun bayyana sauya shekar tasu ne a taron yakin neman zaben Gwamna Bala Mohammed da yammacin ranar Juma’a a Kafin Madaki hedikwatar karamar hukumar Ganjuwa ta jihar.
Masu sauya shekar sun zargi Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Halliru Jika da rashin cika kokarin Gwamna Mohammed ta hanyar samar da ayyukan yi tun daga gwamnatin tarayya zuwa shiyyar su domin bunkasa jihar cikin sauri.
A wani labarin kuma,Garin Ilorin Ya Sami Ruwan Sama Na Farko A Wannan Shekarar
A ranar Asabar ne aka samu ruwan sama na farko a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito.
Ruwan sama ya kawo dauki ga mazauna babban birnin jihar bayan da aka shafe kwanaki ana fama da tsananin zafi.