Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a majalisar wakilai ta kasa Honarabul Nasir Ali Ahmed a ranar Talata ya kaddamar da cibiyar kiwon lafiya matakin farko ta miliyoyin naira a unguwar Gigiyun dake mazabar sa.
A cewar dan majalisar wakilan, Nasir Ali Ahmed, ya bayyana aniyarsa ta gina PHCs a dukkan mazabu 11 na karamar hukumar Nasarawa, wanda daga cikin aka kammala guda 5.
KU KARANTA KUMA Sakacin Wani Likita ya Janyo Rubewar Hannun Jariri a Kano
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Ahmed ya ce baya ga gyaren sashen kula da lafiya matakin farko na gundumar Gigiyun, an kuma gina dakin haihuwa a asibitin.
“A cikin alkawarin da na yi wa mazaba ta, duk mace mai ciki da ta haihu a PHC tana da hakkin Naira 5,000 kuma haihuwa ga kowace mace kyauta ne,” in ji Nasir Ali Ahmed.
“Na kuma kammala shiri da hukumar NYSC na samar da likitoci biyu ga kowanne daga cikin asibitocin a mazabata kuma ni ne zan biya su alawus din su.”
”An samarwa PHC da wata hanyar samar da wutar lantarki ta daban don hana katsewar wutar lantarki, wato hasken rana da firji na musamman don adana alluran rigakafi”.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa, Dan majalisar da ke neman sake tsayawa takara ya ce duk wadannan da sauran su an yi amfani da su wajen inganta hanyoyin samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a mazabar sa.
Akwai hotuna a kasa duba
A Wani Labarin Kuma Karancin Man Fetur: Kamfanin NNPCL Ya Fara Samar Da Man Fetur Ga IPMAN
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Kasa IPMAN, ta ce mahukuntan kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) sun ware wa mambobinta man fetur kai tsaye domin saukaka karancinsa da ya addabi Najeriyar.
Mista Chinedu Okoronkwo, shugaban IPMAN na kasa, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Talata a Legas.