By Ishaq Dabai
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, tare da karamin Ministan ma’adinai Dakta Ichechukwu Sampson Oga sun jagoranci aza harsashin gina kasuwar Zinare wato (Gold Souk) a Garin Batakaye, dake karamar Hukumar Kumbotso.
Gwamnan yace za’a gina wannan kasuwar ne dan bunkasa harkar Kasuwanci a ciki da wajen jihar kano don samarwa da matasa aikinyi tare da karin samun kudaden shiga ga gwamnati dan ciyar da jihar gaba.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewar Allah ya albarkaci Jihar Kano da dimbun ma’adinai daban-daban, inda ya tabbatar da bayar da cikakken goyon bayan Gwamnatin sa domin samun nasarar kammala aikin.
Yayin gudanar da taron, Gwamnan yana tare da kwamishinan kasuwanci, Barista Ibrahim mukhtar da mai baiwa Gwamnan shawara akan harkokin ma’adinai, Hajiya Balaraba Ibrahim Ahmed da sauran jami’an Gwamnati.