Hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano ta rufe wasu shaguna a kasuwar Kantin Kwari sakamakon samun su da yin ha’inci a kasuwancin su.
Hukumar karkashin jagorancin Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya ta rufe shagunan ne biyo bayan kin amsa gayyatar da hukumar tayi musu sakamakon zargin da ake musu na rashin cika adadin yadi yayin da suke sayarwa da al’umma.
Tun da fari dai hukumar ta samu rahoton cewa wadannan batagarin ‘yan kasuwa suna sayar wa da mutane yadi ashirin da tara ko da takwas ko ma kasa da haka a matsayin bandir guda mai yadi talatin, ko kuma yadi tara a matsayin yadi goma da suran su.
Bayan bincike hukumar ta gayyaci wadansu ‘yan kasuwar da abin ya shafa don tattaunawa da su akan al’amarin yayin su kuma suka ki amsa gayyatar wanda hakan ya jawo hukumar ta rufe musu shagunan.
Shugaban hukumar Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya ya yi gargadi ga ‘yan kasuwa masu irin wannan dabi’a ta cutar al’umma da su daina domin hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin da ya dace akan duk wanda aka samu da laifin yin hakan.
Ya kuma jaddada yin Kira ga al’ummar jihar Kano da su cigaba da bai wa hukumar rahoto mai gamsarwa akan irin wadannan batagarin ‘yan kasuwa.
Wuraren da abin ya shafa sun hada da shaguna a layin inyamurai da gidan Danfas da gidan Mudan da gidan Zainab da gidan Zita da gidan Mr Zhou da sauran su.