A ranar Larabar da ta gabata ne Kotun Majistare da ke Jihar Kano, karkashin jagorancin Alkalin Kotun Mai shari’a Farouk Ibrahim Umar, ta yanke wa wani mutum mai suna Aliyu Yahuza mai shekaru 20 da kuma wasu mutane biyu hukuncin daurin watanni bakwai a gidan gyaran hali, bayan da aka same su da laifin aikata zina.
Wadanda ake tuhumar suna zaune a Goron Dutse Quarters Kano, an yanke musu hukunci ne da laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma zina.
Alkalin Kotun Mai shari’a Farouk Ibrahim Umar ya yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin watanni bakwai a gidan yari, da aiki tukuru ko kuma su biya tarar Naira 20,000 bisa aikata laifin zina.
Kazalika, Ibrahim Umar ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin bulala 12 bisa laifin hada baki.
Mutanen ukun da aka yankewa hukuncin sune Aliyu Yahuza mai shekaru 20 da Amir Rabiu mai shekaru 19 da kuma Musa Gambo mai shekaru 19.
Tun da farko, mai gabatar da kara, Mista Auwalu Dandago, ya sanar da kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 13 ga Nuwamban shekarar 2021 a Kofar Waika Quarters, dake Birnin Kano.
Dandago ya ce a wannan rana da misalin karfe 2:00 na rana, wadanda ake tuhumar da laifin hada baki, sun kai yarinyar mai shekaru 14 a wani gida da ke kofar Waika Quarters suka yi lalata da ita daya bayan daya.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 97 da na 387 na kundin laifuffuka na jihar Kano.