Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce dokar hana zirga-zirgar babura a fadin jihar daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe har yanzu tana ci gaba da aiki, inda ta yi kira ga masu hawan doki da su bi wannan umarni. Kamar yadda Daily Trust ta euwaito.
Rundunar ta kuma haramta hawan dokin gargajiya da aka fi sani da Kilisa a cikin watan Ramadan da kuma amfani da wasan wuta a cikin babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fani-Kayode ya yi wani tsokaci, bayan DSS ta bankaɗo shirin kafa gwamnatin wucin gadi
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
“Rundunar da ke aiki tare da sauran jami’an tsaro aka dora wa alhakin kame masu laifin take wannan doka.
“An hana hawan doki (Kilisa) da amfani da wasan wuta, kuma za a kama wadanda suka karya doka a gurfanar da su a gaban kuliya.
“Ya kamata mutanen da ke halartar Masallaci da wuraren Tafsiri a cikin Watan Alfarma su kasance masu taka-tsan-tsan ta hanyar sanin mutane da abubuwan da ke kewaye,” in ji Kiyawa.
A wani labarin kuma, Rikicin bayan zabe: ‘Yan daba sun kai hari kan ‘Ya’yan Jam’iyar PDP, Da Fada
Rikicin bayan zabe ya barke a wasu sassan jihar Ogun a halin yanzu, yayin da wasu ‘yan daba suka kai hari kan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da wata Fadar masarautar gargajiya dake jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An kai hare-haren ne a wasu yankunan kananan hukumomin Ikenne da Remo ta Arewa da kuma Sagamu na jihar Ogun.