Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya umarci dukkanin kwamandojin soji da sojoji da su dauki fansa kan mutuwar abokan aikinsu wadanda yan fashion daku suka kashe a yankunan Zungeru da Shiroro.
Da yake jawabi yayin jana’izar sojojin da yan bindiga suka kashe a jihar Neja a ranar Juma’a, hukumar CDS ta sha alwashin cewa wadanda suka aikata wannan aika-aika za su fuskanci hukunci daidai da abinda duka aikata.
Kalamansa sunce Lokacin da za ku binne naku, kuna jin zafi sosai. Ina so in tabbatar wa iyalai cewa mutuwar su ba a banza ba ne.
Muna godiya gare su za mu tabbatar da wadanda suka yi haka dole ne su biya wannan. Ina amfani da wannan damar wajen kira ga dukkan kwamandoji da sojoji a duk fadin Najeriya cewa dole ne mu dauki fansa. Wadanda suka yi haka da wadanda ke ci gaba da kashe mutanenmu a duk inda suke za mu fitar da su.
KARANTA NANAn Samu Asarar Rayuka Yayinda Jirgin Ruwa Ya Kife A Jahar Nasarawa
Ya ba da tabbacin cewa sojoji za su bi sahun yan fashi yan ta’adda, da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka a fadin kasar nan domin tabbatar da an kawo su gaban hukuma an hukunta su daidai da abinda suka aikata
A satin da ya gabata ne wasu gungun yan bindiga daji suka harbe wani jirgi a karamar hukumar Shiroro jahar Neja dake Arewa ta tsakiyar Najeriya.
Sai kuma a karamar hukumar Zungeru duk dai a jahar ta Neja inda yan bindiga suka bindige Sojoji takwas har lahira,abinda ya sa shakku a cikin zukatan al’ummar Najeriya.
A WANI LABARIN KUMA
Kar Ku Bata Mana SunaTa Hanyar Karbar Cin Hanci Da Rashawa-IGP Ga Yan Sanda
Mukaddashin shugaban hukumar yan sanda ta Najeriya Olukayode Egbetokun yayi kira ga jami’an yan sandan kasar da su daina karbara cin hanci daga mutane domin hakan na matukar zibad da Kumar hukumar a wajen al’ummar kasar.