Likitocin asibitoci a kasar Ingila a ranar Juma’a sun sanar da shirin su na fara yajin aikin mafi dadewa a tarihin hukumar kula da lafiya ta kasar, wadda ke samun tallafi daga Gwamnatin kasar.
Wannan dai na a matsayin ci gaba da takun saka tsakanin ma’aikatan lafiyar kasar, da kuma gwamnati kan batun biyan su albashi.
KU KARANTA: Kano: Dubun Wani Lauyan Bogi Ta Cika, Bayan Bayyana Gaban Alkali
Ƙananan likitoci da kan taimaka da duba marasa lafiya, za su tafi yajin aikin na kwanaki biyar daga karfe 7:00 na safe (0600 GMT) a ranar 13 ga Yuli har zuwa ranar 18 ga Yuli, in ji kungiyar likitocin Burtaniya.
Cimma wannan matsaya ta bai daya, ta biyo bayan cikar NHS shekaru 75 a wannan watan, kuma hakan ya sanya aka samu masu yajin aikin gargadi na awanni 72, don adawa da kin amincewa da gwamnati ta yi kan tayin karin albashin kashi biyar.
Likitoci sun ce an samu raguwar kashi 26 cikin 100 na albashin ma’aikata a cikin shekaru 15 da suka wuce, saboda albashin ya kasa tafiya daidai da hauhawar farashin kayayyaki.
Suna son a maido da albashin zuwa matakin 2008-2009 amma gwamnati ta ce hakan na nufin za a ba da albashi kusan kashi 35 cikin 100 a bana kuma yana da tsada sosai.
Robert Laurenson da Vivek Trivedi, wadanda suka hada gwiwa da shugaban kwamitin kananan likitocin BMA, sun ce da alama gwamnati ta yi niyyar barin NHS ta kama layin wargajewa.
A wani labarin kuma: Najeriya ta Nemi Taimakon Majalisar Dinkin Duniya Domin Yakar Yan Ta’adda
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da takwarorinsu na ci gaban kasashe, da su karfafa goyon bayan aiwatar da dabarun yankin tafkin Chadi.
A cewar gwamnatin hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, fargadowa da kuma juriya, daidai lokacin da yankunan ke fama masu aikata ta’addanci.
Babban jami’in kula da harkokin yaki da ta’addanci na kasa (NCTC), ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA), Rear Adm. Yaminu Musa mai ritaya, ya yi wannan kiran a taron makon yaki da ta’addanci karo na 3 na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York.