Karancin Naira: Shaiɗan ne ya aiko Emefiele domin ya azabtar da ƴan Najeriya – Jigo a APC
A ranar Juma’ar da ta gabata ne tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele a matsayin wanda shaidan ya aiko domin azabtar da ‘yan Najeriya.
Fani-Kayode ya ce nan ba da jimawa ba Shaidan zai yi watsi da Emefiele.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dabarar Da Na Yiwa Malamin Da Yake Son Yayi Lalata Da Ni -Wata Ɗaliba
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, jigo a jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya rubuta: “Godwin, Shaidan ne ya aiko ka don ka azabtar da Najeriya. Kai dan iska ne kuma dabba.
“Shaidan da ke amfani da ku zai yi watsi da ku nan ba da jimawa ba ya jefa ku kamar takardar bayan gida. Bayan haka al’ummar Najeriya za su fatattake ku da rai su sanya ku biya ku da laifin cin zarafin bil’adama.”
Jigon na jam’iyyar APC ya koka akan gwamnatin tarayya na kin amincewa da bukatar kotun koli.
“FG ta yi biyayya ga umarnin Kotun Koli kuma ta bayyana cewa tsoffin takardun Naira sun ci gaba da zama a kan doka sai dai idan kotu ta ce akasin haka. Mun ci nasara,” ya rubuta.
Emefiele dai ya sha suka daga ‘yan Najeriya kan karancin kudin da ake fama da shi na Naira bayan sake fasalin takardun kudi na N200, N500, N1000.
Duk da kokarin da babban bankin na CBN ya yi na dakatar da zagayawa tsofaffin kuɗin, kotun koli ta dakatar da gwamnatin tarayya daga dakatar da amfani da tsofaffin takardun daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
A wani labarin kuma: Na yi nadamar marawa Atiku baya a 2019 – Fayose
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce a bar tsofaffin takardun kudi na Naira su yi aiki tare da wadanda aka canja.
Lawan ya bayyana haka ne yayin da ya ke bayyana cewa babu bukatar wani lokaci kan sahihancin kudin tsohon naira.