Karanta Jerin ma’aikatun da suka fi samun kasafin kuɗi a 2024
Ma’aikatar tsaro ta samu kaso mafi tsoka – da Naira tiriliyan N1.3tn a cikin kasafin shekarar 2024 da aka amince da shi.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito a ranar Asabar cewa, an samu karin kudirin kasafin kudi daga majalisun dokokin kasar biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin shugabanci da munanan manufofi ne ke cutar da Nijeriya – APM
Majalisar ta kara kasafin kudin da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da kudi naira tiriliyan 1.2.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Abubakar Bichi, ya shaida wa manema labarai a karshen zaman na musamman a ranar Asabar din da ta gabata cewa, an samu karin Naira tiriliyan 1.2 ne saboda hauhawar farashin kayayyaki, da kuma alkawarin da Kamfanonin Gwamnati, GOEs suka yi na kara musu kudaden shiga. .
A cikin kasafin kudin da aka amince da shi, DAILY POST ta ruwaito cewa ma’aikatar tsaro ta samu kaso mafi tsoka na Naira tiriliyan N1.3tn.
Sannan kuma ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta biyo ta da Naira biliyan N869.121bn.
Ma’aikatar ilimi ta samu Naira biliyan N857.134bn.
Ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a – ta samu Naira biliyan N667.577bn.
Ma’aikatar Cikin Gida – N362.552bn.
Ma’aikatar Matasa – N201.467bn.
Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro – N199.763bn.
Ma’aikatar Harkokin Waje – N140.456bn.
Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci – N110.248bn.
Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya – N100.248bn.
Fadar Shugaban Kasa – N97.913bn
A wani labarin kuma:Majalisar Dattawa Ta Yi Makokin Na’Abba A Gaban Majalisa
A ranar Asabar din da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta yi zaman makokin tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, wanda ya rasu ranar Laraba a Abuja yana da shekaru 65 a duniya.
Majalisar koli ta kasa yayin zaman ta na ranar Asabar ta yi shiru na minti daya biyo bayan kudirin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya gabatar kan rasuwar Na’Abba.