Karbar hatsi daga Ukraine ba gazawa ba ne ga ƙasar nan, in ji gwamnatin Najeriya
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris, ya ce kasancewar Najeriya ta karbi hatsi daga kasar Ukraine, ba zai sa Najeriya ta zama kasa mai rauni ko kasawa ba.
“Masar na samun kusan kashi 60 na hatsin da take samu daga Ukraine. Kasancewar Masar na samun kusan kashi 60 cikin 100 na hatsin da take samu daga Ukraine bai sa ta zama ƙasa ta kasa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Aiwatar da yarjejeniya ne kawai zai dakatar da yajin aikin fadin kasar nan – Inji NLC
“Gaskiya cewa muna fuskantar kalubale a halin yanzu bai sa Najeriya ta zama kasa ta kasa.
“Saboda haka karbar hatsi daga Ukraine ba zai sa Najeriya ko Masar ta kasa ba.
“Abu ne na al’ada, saboda akwai kasashe su dogara da juna,” in ji Ministan a taron shekara-shekara na jagoranci da lambar yabo ta 2023 a ranar Talata a Abuja.
Kamfanin Leadership, masu buga jaridun Leadership ne suka shirya taron.
A cewar ministan, gaskiya ne Najeriya na fuskantar wasu kalubale kuma shugaban kasa Bola Tinubu yana sane da hakan kuma bai yi kasa a gwiwa ba.
“Yan Najeriya sun zabi Tinubu ne da zurfin fahimta da kuma yakinin cewa yana da karfin da zai iya juyar da al’amura zuwa ga kyau; kuma abin da yake yi kenan
A wani labarin kuma:Dalilin da yasa Kotu ta hana Hukumar yaƙi da cin hanci binciken Ganduje
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ba ta da hurumin binciken tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje kan faifan bidiyon na karbar cin hancin Dala miliyan 5.
Alkalin kotun, Mai shari’a Abdullahi Liman, a lokacin da yake yanke hukuncin a ranar Talata, ya ce laifin da ake zargin laifin tarayya ne wanda babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC za ta iya gurfanar da shi.