Hukumar KAROTA tayi nasarar Damke wani matukin Adai-daita Sahu Abdullahi Baba-kura bisa zargin yin amfanin da dan sahunsa wajen satar wayoyin jama’a.
Wanann na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar ranar Litinin, tare da rabata ga manema labarai.
Nabulisi Kofar Na’isa ya ce matashin dan asalin garin Maiduguri ne da ake sana’ar Adadidaita Sahu a Kano.
Ya ce jami’in hukumar ne suka kamashi a bakin tashar motar ‘Yankaba ranar Asabar din da ta gabata, jim kadan bayan wani magidanci ya nemi taimakon jami’an hukumar kan dan sahun.
Magidancin ya ce bayan saukarsa daga Adai-daita Sahun mutumin ne ya fahimci sun dauke masa wayarsa ya yin da ya ke cikin baburin.
Hakan ya sa jami’an KAROTA suka cafke shi, tare da bincikarsa inda Kuma suka same shi da wayoyi guda uku kirar androad.
A binciken da Hukumar KAROTA ta gudanar ta gano Babakura na amfani da shigowar baki da ke sauka a tashar motar Yankaba domin aikata muguwar sana’arsa.
Tuni dai Hukumar ta mika shi ga rundunar Yan sanda ta jihar Kano domin fadada bincike.