Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da baiwa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum kyautar lambar girmamawa ta CON (Commander of the Order of Niger).
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aikewa gwamnan.
“Ina farin cikin sanar da kai cewa, Shugaban Tarayyar Najeriya, Mai Girma Muhammadu Buhari, GCFR, ya amince da karrama ka na kasa, a matsayin CON (Commander of the Order of the Niger)”, Akume ya rubuta.
KARANTA KUMA: Zulum Adalin Shugaba Ne Abun Koyi, Inji Buhari
Ministan, a cikin wasikar mai kwanan watan 19 ga Satumbar 2022, mai lamba Ref: FMSDIGA/NHA/001k/T/90, ya ce za a gudanar da bikin karramawar da safiyar Talata, 11 ga Oktoba, 2022, a Cibiyar Taro ta Duniya (ICC) a Abuja.
A ranar 28 ga watan Agusta, 2021, Shugaban kasar Nijar Mohammed Bazoum ya baiwa Gwamna Zulum kyautar lambar girmamawa ta kasa ta biyu, “de Grand Officer Dans I`Ordre”, wanda yayi daidai da Grand Commander of the Order of the Niger. GCON, a cikin jadawalin karramawar kasa a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Zulum yana da kyaututtuka sama da 20, yawancinsu daga manyan jaridun Najeriya; ƙwararrun ƙungiyoyi da cibiyoyin ilimi, waɗanda suka haɗa da Jami’ar Ibadan, Kwalejin Kiwon Lafiya ta ƙasa, Jami’ar Afe Babalola, Ado Ekiti, da sauransu.
A wani labarin kuma: Abin da Wike Ya Fadawa Atiku A Wani Sabon Taro Akan Rikicin PDP
A ci gaba da kokarin sasanta rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya sake ganawa da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Wata majiya mai tushe a wajen taron ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa wasu manyan hadiman biyu sun halarci taron.