Kimanin masu harkallar karuwanci su 50 ne aka kama a Koforidua, da ke Ghana, in ji GhanaWeb.
DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Wani dan majalisar wakilai mai wakiltar New Juaben ta kudu, Michael Baafi, da ‘yan sanda ne suka fara aikin.
A cewar wata majiya, wasu daga cikin mutanen da aka kama a gidajen karuwai a sassan karamar hukumar New Juban ta Kudu da aka yi safarar su ‘yan Najeriya ne.
KARANTA WANNAN Yadda ‘Yan Mata Ke Kara Shiga Harkar Karuwanci
Baafi ya tabbatar da kamun ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Yunin 2023, lokacin da yake magana a Cibiyar Bauta ta Duniya ta Fentikos da ke Koforidua don kammala bikin makon matasa na kasa da Cibiyar ta yi.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Gidauniyar Mastercard tana shirin samar wa ‘yan Najeriya guraben ayyukan yi miliyan 10 nan da shekarar 2030
Ya ce, “Na umurci ‘yan sanda da su gudanar da wani sumame domin kamo duk wasu karuwai da suka zo garinmu jiya kuma ‘yan sandan tsakiya suka je da misalin karfe 1:00 na dare.
“Sun yi nasarar kama kusan mutane 50. Zan tabbatar gobe za su gurfanar da su a gaban kotu kafin in tafi.
“Kusan kashi 99 cikin 100 ‘yan Najeriya ne kuma suna zuwa nan ne domin su tona asirin Koforidua. Duk wanda ke yin wannan kasuwancin ba za a yarda da shi ba.
“Idan kun san mutane a kowane wuri, ghetto, gida ko wasu masu zaman kansu, kuma idan ba za ku iya zuwa ofishin ‘yan sanda ba, ku kira ni.” Kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
A Wani Labarin Kuma Manyan Nasarorin MOPPAN A Watanni 18 Na Jagoranci Dr. Sarari
An gudanar da taron babbar kungiyar masu ‘yan fim a ranar Asabar 10 ga Yunin 2023 kungiyar MOPPAN ta kasa ta gudanar da taronta na karahen shekara, inda ta gayyaci dukkanin shugabanni a matakai daban-daban na kasa daga jihohi.
Taron, wanda ya gudana a babban dakin taro na Kannywood TV da ke Tudun Yola a birnin Kano, ya kafa babban tarihi a masana’antar shirya finafinan Hausa.