Tsohon Kocin ‘yan wasan kwallon kafa ta Nijeriya, Christian Chukwu ya karyata labarin mutuwarsa da wadansu kafafen watsa labarai suka yada, inda ya ce yana nan cikin koshin lafiya.
Christian Chukwu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a hirar da ya yi da majiyarmu a gidansa dake Trans Ekulu dake jihar Inugu.
A ranar 8 ga watan Janairun 2021 ne labari ya cika da cewa Christian Chukwu ya mutu. Sai dai tsohon kocin Nijeriyar ya ce ya yi taron cikarsa shekaru 70 a duniya a ranar 4 ga watan Janairun 2021. Inda ya nuna mamakinsa na yadda wasu suka yada karyar ya mutu.