A kalla mutane takwas ne suka gamu da ajalin su a wani harin kan mai uwa da wabi da wani matashi ya kai a birnin Indianapolis na kasar Amurka.
Yan sanda sun bayyana cewa matashin ya fara harbin kan mai uwa da wabin ne bayan fitar shi daga motar da ya zo daidai gurin da abin ya faru.
To sai dai mintuna bayan wannan aika-aika, dan ta’addan ya Hallaka kan shi gabannin zuwan yan sanda, ko da yake har kawo yanzu ba a gano matashin ba.
Wannan shine hari mafi muni da aka kai kasar Amurka a yan baya-bayan nan da ya yi sanadin mutane da dama.
Wannan Hari ya auku ne wuraren karfe 11 na dare wato karfe uku daidai agogon GMT a birnin na Indiana.
Tuni gwamnan jihar Joe Hogsett ya kai ziyarar ta’aziyar shi tare da kiran Amurkawa da su tashi tsaye wajen ƙoƙarin dakile hare haren ta’addanci.