Ana zargin kasar Seychelles da kakaba takunkumi ga masu rike da fasfo na Najeriya, da neman biza na wucin gadi ko hutu, Vanguard ta rawaito.
Wani mai yin balaguro, ya ankarar a yammacin ranar Asabar bayan ya karɓi imel ɗin kin amincewa.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Yari Ya Shaki Iskar ‘Yanci daga Hannun DSS
Hoton wanda aka yada a shafin Twitter a wani bangare na cewa, “Muna nadamar sanar da ku cewa an ki amincewa da bukatar ku, kamar yadda dokar shige-da-fice ta tanada.
“A yanzu ba ma karbar duk wani mai fasfo na Najeriya don yin hutu. Da fatan za a tuntuɓi wannan shafi na shige da fice na Seychelles http://www.ics.gov.sc/ ko kuma a kira wannan lambar 248 4 293 636 don neman ƙarin bayani.”
Mai amfani ya ce, “Da alama Seychelles ta sanya dokar hana masu fasfo na Najeriya.
“Wanda yake da fasfo na Najeriya shine zaku iya jinkirta shirin tafiya har sai kun zama Bill Gates, sannan kuma manufofin shige da fice zasu zama kamar wasan Dey.”
Haramcin ya zo ne watanni shida bayan Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye da kasar.
Kafin dakatarwar dai, Najeriya ta dade tana kulla yarjejeniya ba tare da biza ba da kasar Seychelles wadda ta baiwa ‘yan Najeriya damar shiga kasar ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 30.
A wani labarin kuma,Wasu Fusatattun ’Yan Daba Sun Farmaki Sakatariyar Yakin Neman Zaben Gwamnan Jam’iyyar SDP
Wasu fusattatun ‘yan daba sun kai hari a sakatariyar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar SDP Muritala Yakubu Ajaka a safiyar Lahadi.
Fusatattun ‘yan dabar sun lala gaban ofishin sakatariyar da gilasan dake jiki a daidai lokacin da suka ciro tutocin shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu da aka lika a bangon Sakatariyar suka kone su kurmus a kofar ofishin.