Kashe-kashen da a ke yi a Arewa-maso Yamma ya fi na Arewa maso Gabas — Cewar El-rufa’i
Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna a yau Alhamis ya ce girman kalubalen tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa-maso-Yamma ya fi wanda a ka gani a Arewa-maso-Gabas.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Giwa na jihar Kaduna, inda ‘yan ta’adda su ka addabi mutanen ya kin kwanaki biyar da su ka gabata, inda a ka kashe ko kuma sace mutane da dama.
A cewarsa, noma ya zama ba zai yiwu ba, yayin da ake asarar rayuka sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan ta’adda sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin jirgin ƙasa da su kai garkuwa da su
“Muna ta matsa lamba tun shekaru biyu da suka gabata cewa sojoji daga sama su riƙa jefo bamabamai, inda su kuma sojojin ƙasa su riƙa harbe duk wani wanda ya tsere wa bam din a dazuka.
“Ban yarda cewa akwai wani marar laifi a cikin dajikan ba.
“Na yi niyyar na ga shugaban kasa domin na sake nanata hakan kuma in nemi a kafa shelkwatar rundunar soji sabo da yankin Arewa-maso-Yamma,” “in ji shi.
“Lokaci ya yi da sojojin saman Najeriya da sojojin Najeriya za su ba wa ‘yan ta’adda bama-bamai ba tare da wanzuwa ba.
“Tare da sanarwar da babbar kotun tarayya ta bayar na cewa wadannan ‘yan ta’adda ‘yan ta’adda ne, akwai bukatar hukumomin tsaro su dauki tsauraran matakai domin ganin an kawo karshen wadannan barayin,” in ji Mista El-Rufa’i.
Ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Giwa sakamakon harin ƴan ta’adda da ya addabe su tsawon kwanaki biyar.