Tsohon Sanatan Najeriya Ben Murray-Bruce ya koka yadda ake samun ƙaruwar tsafe-tsafe a tsakanin matasa.
Tsohon Sanatan a kafar Twita a ranar Lahadi, yace matasa wanda ya kamata su zama “Shuwagabanni na gobe amma suna cigaba da aikata ayyukan ta’addanci domin su zamanto masu kuɗi a dare ɗaya.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Maroko ta girgiza bayan Mutuwar Wani ‘Karamin Yaro Rayan’
“Mike damun matasa ne, wanda suka yi imani da kashe mutane domin su zamanto masu kuɗi” inji shi.
“Ƴan Najeriya da dama ana rasa su kullum, inda ɓa’a gano wasu. Wasu ana samun su matattu da wani sashe nasu babu. Dole mu magance wannan matsalar.”
Yace “talauci da rashin aikin yi yana sanyawa matasa suna aikata ayyukan tsafi ta hanyar kisa”bazamu taba yarda ba.
Domin magance matsalar, Murray-Bruce yace iyalai dole su cigaba da yiwa ɗiyan su tarbiyya ta gari.
“Dole mu dawo da ɗabi’un mu nads, inda tarbiyya ke farawa daga gida.