Kashi 70 na yaran Makaranta ba sa Ɗaukar abinda a ke koya musu — Inji UNICEF
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kashi 70 cikin 100 na yaran da ke makarantu ba sa ɗaukar abinda a ke koya musu, inda ta ce ya zama tilas masu ruwa da tsaki su magance haka.
Kwararre a fannin Sadarwa a UNICEF, Geoffrey Njoku, ne ya bayyana haka a Kano a yau Juma’a a taron tattaunawa na kwanaki biyu kan kafafen yada labarai kan muradun ci gaba mai dorewa, SDGs.
Njoku ya ce babu wata kasa da za ta cimma nasarar SDGs din ta in har za ta kau da kai kan hakkin yara, yana mai cewa dole ne masu ruwa da tsaki su fara mai da hankali kan SDG a matsayin hakkin yara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Direban tasi zai shafe watanni 30 a gidan yari a dalilin kaɗe ƴar sanda da mota
A cewarsa, dole ne a maida hankali a kan wani fanni na ilimi, wanda shi ne tushen karance-karance da lissafi.
“Tun daga shekarar 2010, mun matsa kaimi wajen sauya labarin yara miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta, amma ko a wancan lokacin kashi 70% na wadanda ke makarantun ba sa ɗaukar abinda a ke koya musu
“Muna bukatar shigar da wadannan kashi 70% a makarantu na yaran da ba sa koyo cikin yara miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta domin a ba su kulawar da ta dace.
“Don haka lokaci ya yi da za mu mai da hankali kan koyo ta hanyar sabunta tsarin ilimi ta hanyar horar da malamai, canza tsarin karatu da samar da hanyar ingantaccen ilimi,” in ji shi.