A ranar Lahadin nan ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bar Najeriya domin ya wakilci shugaba Bola Tinubu a wajen taron 3rd Belt and Road Initiative (BRI) a birnin Beijing na kasar Sin, wanda zai gudana daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Oktoba.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Stanley Nkwocha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi.
Nkwocha ya ce Shettima zai bi sahun shugabannin duniya daga kasashe sama da 130 na Afirka, Asiya, Turai da kuma Latin Amurka don yin shawarwari kan taken, Hadin kai mai inganci da hadin gwiwa Tare don ci gaba da wadata.
Karanta nanJirgin Sojoji Yayi Barin Wuta A Dazukan Borno Da Zamfara Ya Tarwatsa Barayi
A cewarsa, ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai amfani Najeriya bisa tsarin da dandalin ya samar don jawo hankalin masu zuba jari don kara ayyukan raya kasa.
Nkwocha ya kara da cewa mataimakin shugaban kasar zai gana da wasu shugabannin kasashen duniya domin inganta huldar kasuwanci da zuba jari a Najeriya bisa tsarin bunkasa tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.
A wani labarin kumaBa’a Fita Wata Ba:Barayi Sun Kuma Sace Dalibai Biyu Na Jami’ar Tarayya Dake Gusau
Bugu da kari taron na BRI na shekarar 2023, zai cika shekaru 10 da kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranta, a matsayin wani shiri na dabarun raya ababen more rayuwa na duniya, wanda gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta dauka tare da kaddamar da ita.