By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta samu nasarar fatattakar ‘yan ta’adda a wasu hare-hare guda uku tare da kubutar da wasu mata uku da kuma dabbobi da dama bayan da suka samu kiran kai hari a kauyen Garin Zaki da ke karamar hukumar Batsari a jihar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Afrilun 2022, inda wasu ‘yan fashin daji dauke da makamai a kan babura suka afkawa al’ummar garin inda suka yi ta harbe-harbe kafin su yi awon gaba da matan uku tare da yin awon gaba da wasu dabbobin gida.
Da samun sanarwar harin, jami’in dan sandan yankin ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa yankin, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan da wasu manyan bindigu tare da kubutar da uku daga cikin matan da aka yi garkuwa da su da shanu 15 na mutanen kauyen. .
A wannan rana jami’an ‘yan sanda a jihar sun kuma dakile wani harin da aka kai kauyen Kadage da ke karamar hukumar Kurfi inda suka yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan fashin tare da kwato makamin AK-47 da dukkan dabbobin da aka sace.
An ce da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga.
A wani harin makamancin haka, SP Gambo ya ce rundunar ta samu nasarar kwato bindigu kirar AK 47 guda biyu da alburusai 11 na milimita 7.62, dangane da wani lamari da ya faru a ranar 21 ga watan Afrilun 2022 a kauyen Tsamiyar Gamzako da ke karamar hukumar Kafur ta jihar inda wasu ‘yan ta’adda biyu suka kai harin. An kuma kwace bindiga kirar AK 47, da kuma wasu bindigogi na gida guda biyu.
Kazalika, A ranar 26 ga watan Afrilu, 2022, SP Gambo, ya ce ‘yan sanda sun samu kiran waya cewa ‘yan fashin daji da yawansu, dauke da bindigogi kirar AK 47 sun kai hari kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana ta jihar. Sakamakon haka, DPO Safana, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da na ‘yan banga zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan fashin daji tare da samun nasarar kwato bindiga kirar AK 47 daya da babura guda biyu na maharan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda, ya yabawa kokarin ‘yan sanda da ‘yan banga wajen dakile ‘yan ta’addan.
Yayin da yake tabbatar wa da jama’a cewa ‘yan sanda za su ci gaba da tunkarar ‘yan ta’addan da ba su da ra’ayin rikau har sai an gurfanar da su a gaban kotu, CP Dabban ya bukace su da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba su bayanai masu amfani da za su taimaka musu.