Kayayyakin jabu sama da Miliyan 100 na jiran ƙonawa a Kano
Hukumar Kare Kayayyakin Kasuwanci ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta kwace kayayyakin jabu, dana mazantaka da marasa inganci da suka kai sama da Naira miliyan 100 a cikin watanni uku da suka wuce.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abokin Amaechi Ya Koma PDP, Duk Da Yunkurin Wike Na Haɗa Kai Da Shugabannin APC
Shugaban riko na Hukumar, Baffa Babba Dan’agundi, ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa Hukumar ta fara bin doka da oda da zai kai ga lalata kayayyakin.
Ya jera wasu kayayyakin da aka kwace da suka hada da gurbatattun takin zamani, fulawa, dabino, shinkafa, spaghetti, madara da kuma semolina.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a watan da ya gabata ne hukumar ta sanar da gano takin zamani mai dimbin yawa a wurare biyu a jihar sannan ta kuma kama wata tirela mai dauke da man semolina da ya kare a babbar kasuwar Mawaka da ke cikin birnin Kano.
Ya kara da cewa an kama mutane 11.
Sai dai ya koka da cewa hukuncin da aka tanadar a cikin dokar da aka kafa hukumar ba ta da tsauri da za ta iya kawo cikas, inda ya bukaci a sake duba ta.