Daruruwan yan keke NAPEP ne suka ki fita aiki a yau a birnin Maiduguri sakamakon cin zarafi da suke zargi hukumomi ke yi musu.
Wannan ya tilasta jamaa’a kafewa a bakin titi don jiran abin hawa, yayin da dalibai da dama suke tattatki kafin zuwa makaranta.
Daya daga cikin matuka keke NAPEP mai su8na Uman Modu ya bayyana cewa ana karbar naira dari ko wace rana a matsayuin haraji to sai dai idan mutum yab gaza biya a kan lokaci to ana iya cin tara kuma idan bai biya ba ana iya kame Keken shi.
“Suna muzguna mana matuka bisa irin shigar da muke yio, misali idan ka saka riga maras hannu to lashakka a wannan rana ba za su barka ka yi aiki ba”
“Masu Karbar haarajin suna bi ko ina don tambayar lasisin tuki wanda kuma ba aikin su ba ne.”
To sai dai yunkurin da Kamfanin Jaridar Daily Trust ya yi na ji daga bankin hukumomi da ake zargi abnin ya ci tura.
Wannan yajin aiki ya sa ala tilas harkoki da dama na yau da kullum, kamar yaddda wata mai saida abincif a titin na Baga mai suan Amina Saleh ta ce a yau duk kwastotmin ta matuka keke NAPEP sun gaza zuwa sakamokon wannan yajin aiki.
Kazalika wata daliba dake rukunin gidaje na Ibrahim Taiwo ta ce dolen ta sai da ta taka da kafa daga nisan wuri gabannin zuwa makaranta a yau.