Kirsimeti: Gwamnan Bauchi, Mohammed ya jaddada kudirinsa na kare rayuka da dukiyoyi
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Ya yi wannan alkawarin ne a cikin sakonsa na fatan alheri a bikin Kirsimeti na 2023 a ranar Litinin a Bauchi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ban Nemi Shugaban Kasa Ya Sulhuntamu Da Fubara Ba-Wike
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na hada kai da jami’an tsaro domin magance haqiqanin barazanar da ke barazana ga rayuwar jama’a da dukiyoyin ‘yan qasa, ta hanyar samar da kayan aiki da sauran tallafi don gudanar da ayyuka masu inganci na samar da tsaro.
Ya ce “Bari na tabbatar muku da cewa yayin da muka fara wa’adinmu na biyu bayan samun gagarumin goyon bayan ku a zabukan da aka gudanar a farkon wannan shekarar, za mu yi aiki tukuru fiye da yadda muka yi a lokacin mulkinmu na farko don samar da ribar dimokuradiyya.”
Ya jera ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, karfafa tattalin arziki da duk wasu shirye-shiryen da ke da alaka kai tsaye kan kyautata zamantakewa da tattalin arziki a matsayin bangarorin da za su sami ci gaba.
A wani labarin kuma:Kayan tallafi ba za su magance matsalolin Najeriya ba – Kukah ga Tinubu
Bishop Hassan Kukah ya tuhumi shugaban kasa Bola Tinubu kan yaki da cin hanci da rashawa da rashin tsaro, yana mai cewa raba tallafi kuɗi ba zai magance matsalolin Najeriya ba.
Kukah, Bishop na darikar Katolika na Sokoto ya lura cewa “Matsalolin Najeriya sun yi katutu, kuma sun samo asali ne daga al’adar cin hanci da rashawa da ta zama ginshikin gudanar da mulki.”