Kisa: Kotu ta yanke wa Mutane 3 hukuncin Kisa
Wata Babbar Kotu a Jos, Jihar Plataeu, ta yankewa mutane 3 hukuncin kisa, sakamakon kisan wani Joseph Gosum.
Kotun ta kama wadancan da laifi akan shari’ar da aka kawo wa kotu daga Gwamnatin Jahar Plataeu.
Jojin na Kotu ta 3 na Babbar Kotun Jihar a Jos, Mai Shari’a Arum Ashom a lokacin da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, yace Kotun ta kama mutane uku da laifin kisan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar FRSC Ta Karrama Direban Mota Saboda Matukar Bin Ka’idojin Hanya
Kotun ta gano cewa “Samson James, da Emmanuel Jah, da Patrick Nyam a watan Disamba na Shekarar 2015 a Gadabiu ta Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Plateau, sun amince cewa kune kuka haddasa mutuwar Joseph Gosum ta hanyar daɓa mashi wuka.
“Laifin da kuka aikata yana karkashin sashe na 97 na manyan laifuka a karkashin sashe na 221, na Dokar Arewacin Nijeriya, ta 1963.
“Ya zama wajibi ga Kotu idan ta tabbatar da hukunci ba tare da Kokwanto ba. Duk ƙoƙarin wanda ake ƙara na kare kanshi ya cimma tura.
Sannan kotu ta gano cewa ya aikata, to shikenan ta tura shi kisan ta hanyar rataya.
Lauyan masu ƙara Barr Mantu ya yabawa Kotu data yanke wannan hukunci kamar yadda Doka ta tanada.
Shi kuwa lauya mai kare wanda ake ƙara Barr. David Adudu yace zai karanci hukuncin, sannan zai ɗaukaka Shari’a