Tsohon Sanata mai wakiltar jahar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya Sanata Shehu Sani ya mayar da martani kan wasu munanan abubuwan da suka faru a jihar Filato a jajibirin Kirsimeti.
Yan bindiga dai sun kai hare-hare a lokaci guda kan al’umma sama da goma sha biyar a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar a jajibirin Kirsimeti.
Karanta nanAn Bukaci Shugaba Tinubu Da Ya Saka Dokar Ta Baci A Jahar Taraba
‘Yan ta’addan sun kona gidaje daban-daban a daren Lahadi, sannan sun yi awon gaba da kayan gona tare da lalata dukiyoyi yayin da suke yanka mutanen.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Talata, ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television’s Sunrise Daily cewa adadin wadanda suka mutu a harin jajibirin Kirsimeti a jihar ya haura 115.
Sai dai da yake magana kan lamarin, Sani, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya ce ya kalli bidiyon sakamakon kisan gillar da aka yi a Filato, inda ya kara da cewa inda wani jariri ke kuka a bayan gawar mahaifiyarsa ne yafi tayar da hankali.
Ya kuma bayyana wannan lamari mai cike da bakin ciki a matsayin daya daga cikin munanan ayyukan ta’addancin da ya taba gani.
A wani labarin kumaHukumar Yan Sanda Ta Karyata Batun Karbar Naira 2,000 Daga Hannun Masu Neman Aikin
Sani ya rubuta cewa, “Na kalli bidiyon sakamakon kisan kiyashin da aka yi a jihar Filato. Wannan yana daya daga cikin mafi zalunci da munanan ayyukan rashin mutuntaka da na taba gani.
Shin ya kamata mu yi Allah wadai da shi kuma mu nemi adalci ba tare da wata shakka ba ko kuwa mu ci gaba da gudanar da ayyukan kashe-kashen jama’a ta hanyar amfani da ra’ayin addini ko kabilanci.
Yanayin da wani jariri ke kuka a bayan gawar mahaifiyarsa, abin tsoro ne da ya kamata ya dagula lamirin duk wani dan kasar nan mai kishin kasa.