Kogi: Dino Melaye yayi magana kan batun karɓar N3bn daga Atiku, Dangote
Ɗan takarar Jam’iyyar PDP, na gwamna a kogi Dino Melaye, ya karyata rahotannin karbar Naira biliyan 3 daga hannun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da Aliko Dangote domin zaben Kogi.
Melaye ya bayyana hakan ne a wajen liyafar cin abincin dare da mambobin kungiyar yakin neman zaben sa suka shirya a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotu Ta Baiwa Tsohon AGF, Adoke Izinin Tafiya Kasar Waje
Ya bayyana ikirarin a matsayin na hannun masu zagin sa da ke son kawo cikas ga yakin neman zabensa.
A cewar Melaye, rade-radin cewa ya karbi Naira biliyan 1 daga hannun Atiku da kuma Naira biliyan 2 daga hannun Dangote, labaran karya ne da masu cin amana suka yi ta yadawa.
“Daya daga cikin darussan shi ne, gabas yanzu sun fi kowa sanin cewa ba za su iya zama gwamna su kadai ba. Dole ne ku hada kai da sauran shiyyoyi don zama gwamna.
“Darasi na biyu kuma na mu daga yamma ne. A lokaci na gaba, ya kamata mu saurari kalmomin hikima daga dattawanmu ba daga ’yan kasuwa waɗanda saboda son kai da son rai suka haifar mana da matsala ba.
“Saboda a karshen wannan rana, abin da dattawanmu ke cewa wannan zai zama mafi muni (zaben) a gare mu, daga karshe abin ya faru.