Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta musanta rahoton da kafafen yada labarai suka bayar da na cewa ta baiwa Rasha makamai, inda ta kira “marasa tushe”, tare da yin tir da Amurka kan samar da muggan makamai ga Ukraine, in ji kamfanin dillancin labarai na KCNA a ranar Juma’a 23 ga watan Disamba.
Kafofin yada labarai na Japan, Tokyo Shimbun sun ruwaito a baya cewa Koriya ta Arewa ta aika da makamai, ciki har da harsasai, zuwa Rasha ta jirgin kasa ta kan iyakarta a watan da ya gabata kuma ana sa ran karin jigilar wasu kayayyaki a cikin makonni masu zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kamfanin Meta Ya Amince zai Biya Dala Miliyan 725 Don Daidaita Kariyar Sirri
Daga nan ne fadar White House ta fada a ranar Alhamis cewa Koriya ta Arewa ta kammala mika makaman farko ga wani kamfanin soji na Rasha mai zaman kansa mai suna Wagner Group (wanda ke hoton kasa), don taimakawa wajen karfafa sojojin Rasha a Ukraine.
A cewar fadar White House, Wagner ya karbi makamai masu linzami da makamai masu cin dogon zango daga Koriya ta Arewa, ko da yake Wagner Yevgeny Prigozhin ya musanta maganar a matsayin “jita-jita da zato”.
Koriya ta Arewa tare da kasashe kamar Iran, Belarus da Syria sun goyi bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Sanarwar da KCNA ta fitar ta ce, “Rahoton karya da kafafen yada labarai na Japan suka bayar na cewa DPRK ta ba wa Rasha makamai, shi ne mafi karancin jan hankali, wanda bai cancanci wani sharhi ko fassara ba,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar.
Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ba ta yi wata magana kan Wagner ba.
Kakakin Koriya ta Arewa ya ce, “Kasar ta DPRK ta kasance ba ta canja ba, a matsayinta na ka’ida kan batun ‘mu’amalar makamai’ tsakanin DPRK da Rasha wanda bai taba faruwa ba,” in ji mai magana da yawun Koriya ta Arewa, ya kara da cewa Amurka ce ke haifar da zubar da jini da lalata ga Ukraine samar mata da muggan makamai iri-iri”.
A wani labarin kuma, APC Zuwa PDP: Muna Kiyaye Duk Wani Rikicin Zabe, Domin Ha’inci Ne
Jam’iyyar APC mai mulki ta mayar wa wata jam’iyyar adawa ta PDP martani inda ta ce ta kyamaci duk wani nau’i na tashe-tashen hankula da kura-kurai a zaben.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya zargi jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da yunkurin kawo cikas a zaben 2023. PDP ta kuma zargi APC da laifin kai hare-haren da aka kai kan cibiyoyin INEC a wasu sassan kasar.