Babbar kotun tarayya dake zaman ta Abuja, taki amincewa da bukatar gwamnan babban bankin kasa CBN, Mr. Godwin Emefele.
Emefele dai na bukatar kotun ta Sahale masa domin tsayawa takarar shugaban kasa, ba tare da ya ajiye mukaminsa ba, inda ya bukaci kotun ta shigo da Hukumar INEC da kuma babban Antoni na kasa domin bashi kariyar da ta kamata.
A yayin zaman kotun na yau Litinin, Emefele ya ce yana son tsayawa takarar shugaban kasa matakin zaben fidda gwani, kuma baya son ajiye mukaminsa na Gwamnan CBN domin gudun me kaje yazo.
Gwamnan CBN din ta bakin lauyan sa Mike Ozekhome ya shaidawa kotun cewa sashi na 84 (12) na dokar zaben 2022, bai shafi nadin da aka yiwa Emefele ba matsayinsa na gwamna.
Kazalika kotun a hukuncin da ta yanke din ta yi sammacin Ministan Shari’a da Hukumar INEC domin karin haske kan cewa Gwamna Emefele bashi da damar tsayawa takara alhalin yana rike da wannan mukami.