Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Larabar nan ta ba tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha izinin tafiya kasar Amurka don neman lafiya.
Da yake bada izinin, mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci magatakardar kotun da ya ba shi fasfo din tafiya na tsohon gwamnan domin gudanar da ziyarar jinya.
Umurnin Alkalin ya biyo bayan bukatar da wani babban Lauyan Najeriya, Mister Ola Olanipekun ya shigar, inda ya sanar da kotun cewa wanda yake karewa na fama da matsalar rashin lafiya.
Olanipekun ya kara da cewa Okorocha, wanda yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Imo ta Arewa a majalisar dattawa, ba zai yi amfani da wannan doka ba kuma zai dawo kasar domin yi masa shari’a.
Ko da yake, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da Mista Chile Okoroma ya wakilta ta yi kakkausar suka da wannan bukata, sai dai hukumar ta yi kakkausar suka a lokacin da Mai Shari’a Ekwo ya bayyana cewa za a amince da bukatar tare da gargadi.
Yayin da yake amsa bukatar, mai shari’a Ekwo ya umarci Okorocha da ya mayarwa magatakardar kotun fasfo din kasa da kwanaki uku da isowarsa kasar.
Daga nan ne mai shari’a Ekwo ya sanya ranar 7 ga watan Nuwamba domin ci gaba da shari’ar sa kan tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta gabatar masa.